Dalilan Da yasa Jikinku ke yin kaikayi Bayan Kun Yi Wanka

0
353

Mutane da yawa suna fuskantar ƙaiƙayi a jikinsu bayan sun yi wanka, amma ba su san dalilin hakan ba, ko abin da za su yi don hana faruwar hakan. A cewar Healthline, lokacin da jikinka ya fara kaikayin, alama ce da ke nuna cewa wani abu naka ba daidai ba ne, kuma yana buƙatar kulawa da gaggawa da magani. Duk da haka, a cikin wannan shirin namu , zan kawo maku Bayyanai a taƙaice dalilan da ke sa jikinku kaikayi bayan wanka.
1. Idan kukayi wanka kuma fatarku ta fara yi maku kaikayi bayan kun fito daga bandaki, ana iya kamuwa da cutar ta Xerosis Cutis, wato rashin lafiyan da ke da alaka da busasshen fatar jikinku yayyin da ya jike da ruwa har ya Kai ga ruwan ya shiga ya kawar da man da kwayoyin fata ke samarwa, hakan ke sa fatar hannaye da kafafu wanku su yi kaikaiyi.

2. Wani dalili na ƙaiƙayi bayan wanka shine nau’in sabulun da kuke amfani da shi. Wasu sabulun idan aka yi amfani da su kuma ba a wanke su da ruwa mai yawa ba, suna iya sa sinadarin da ke cikin su ya shiga cikin fata ya haifar da kaikayi. Yana da kyau ku tuntubi likitan ku don a ba ku shawara mai kyau akan sabulun da ke da kyau ga fatar ku.

3.kaikayi bayan wanka kuma yana iya zama sakamakon samun Aquagenic Purio, wanda shine yanayin lafiya da ke faruwa a lokacin da kwayoyin fata suka sami ruwa mai yawa da ake amfani da su wajen wanka. Wannan yanayin ba kasafai ba ne, kuma ya kamata ku ga likitan ku don samun magani mai kyau.

Yana da mahimmanci a nemi taimakon likita lokacin da jikinku yafara ƙaiƙayi bayan wanka da kuma samun magunguna masu dacewa da magani daga ƙwararren likita. Haka zalika a kula da tsafta da kuma yin wanka akai-akai da ruwa mai tsabta, da sabulu mai lafiya.

By: Firdausi Musa Dantsoho