Rundunar ‘Yan Sanda a Abuja, ta kame wani jami’in DSS da ya yi sanadiyar harbe wasu a kasuwar Garki Ultra Modern Market .

0
28

Kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya, Haruna Garba, ya bayyana cewa an kama wani jami’in ma’aikatar harkokin tsaro na hukumar DSS da ke da hannu wajen harbi a kasuwa wanda ya yi sanadiyar jikkata mutane da dama tare da kwantar da su a asibiti.

Garba ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi ta wayar tarho a ranar Asabar, inda ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ya musanta zargin cewa jami’in DSS da ya yi harbin na tafiya cikin walwala.

“ A cewar sa Har yanzu jami’in DSS na hannun mu; ba a sake shi ba, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.”

A halin da ake ciki kuma an  tabbatar da cewa wadanda harin da ya rutsa da su a kasuwar, yanzu haka suna samun kulawa a wasu asibitocin Abuja.

Wata mummunar zanga-zanga da ‘yan sanda suka dakile ta ta barke ne a daren ranar Alhamis bayan harbin da wani jami’in DSS ya yi wa wani mai zanen kaya wanda ya  harbe shi ba kakkautawa tare da jikkata wasu da dama.

An samu labarin cewa wani abokin ciniki ya kawo wa madinkin kayan kwalliyar ne bisa zargin kin kai wasu daga cikin kaya a ranar da aka yi alkawari.

Wata ‘yar kasuwa a kasuwar, wadda ba ta son a buga sunanta saboda tsoron kada a kai mata hari, ta ce wasu abokan sana’ar masu zanen kaya da suka samu labarin lamarin ne suka shiga tsakani amma tsangwamarsu bai yi wa jami’an DSS din dadi ba.

A cewarta, jami’an tsaron sun kama shi ne  ja tare da danka  shi a hannun ‘yan sanda bayan da ake zargin ya harbe mai zanen kayan adon.

“Wata abokiiyar cinikin mai zanen kaya ce ta kawo DSS don a cewar ta mai zanen kayan bai dinka kayan ta ba. Batun ya haifar da muhawara mai tsanani. Dan kasuwar ya kara da cewa an kama jami’in DSS, aka tsare shi a ofishin ‘yan sanda na Kasuwar .

Kakakin hukumar ta DSS, Peter Afunanya, a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis din da ta gabatan ya ce rundunar ‘yan sandan sirri na gudanar da bincike kan lamarin.

Ya ce, “An jawo hankalin ma’aikatan gwamnatin tarayya kan lamarin da ya faru ,Saboda haka, Hukumar ta fara bincike kan lamarin. An ba wa jama’a tabbacin cewa za a sanar da su cikakkun bayanai game da lamarin bayan an kammala bincike.

 

Daga Fatima Abubakar.