Biden ya yabawa ‘Karfin Jagorancin’ Tinubu a matsayin Shugaban ECOWAS

0
12

SHUGABA Joe Biden, a ranar Lahadi, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan “karfin shugabancinsa” a matsayinsa na shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS).

Shugaban na Amurka ya yaba da yadda takwaransa na Najeriya ya yi alkawarin kare da kiyaye dimokuradiyya a Jamhuriyar Nijar da ta yi juyin mulki a yankin yammacin Afirka.

Biden ya gana da Tinubu a ranar Lahadi a wajen taron G20 a New Delhi, Indiya kuma ya karfafa jajircewar Amurka ga Najeriya.

“Shugaba Biden ya yi maraba da matakan da gwamnatin Tinubu ta dauka na gyara tattalin arzikin Najeriya, ya kuma gode wa shugaba Tinubu bisa jajircewarsa a matsayinsa na shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka don kare da kiyaye dimokuradiyya da bin doka da oda a Nijar da ma yankin baki daya.” Fadar White House ta ce a cikin wata sanarwa.

“Gayyatar Najeriya zuwa taron G20, amincewa da muhimmiyar rawar da Najeriya ke takawa a duniya a matsayin babbar dimokuradiyya da tattalin arziki a Afirka.”

Firdausi Musa Dantsoho