Shugaban Majalisar Dattawa Abdullahi Yahaya ya canja sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

0
45

Sanata Yahaya Abdullahi, shugaban majalisar dattawa, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP a jihar Kebbi.

Mai baiwa Abdullahi shawara kan harkokin yada labarai Muhammad Jamil Gulma ya tabbatar da sauya shekar a ranar Talata.

“Shugaban majalisar dattawa, Dakta Yahaya Abdullahi a ranar Laraba da karfe 9 na safe zai bar Abuja zuwa Kebbi, ya zarce karamar hukumar Kamba don bayyana shekarsa a matsayin jam’iyyar PDP da kuma nuna sha’awarsa ta tsayawa takara,”.

Yahaya dai ya halarci zabukan fitar da gwani na gwamnan jihar Kebbi na jam’iyyar APC, inda aka ce bai samu kuri’u ba.

Tun daga nan ya yi watsi da sakamakon kuma ya kwatanta shi a matsayin abin shambo da wasan yara.

An tattaro cewa mai yiwuwa sauya shekar tasa ba ta rasa nasaba da zaben fidda gwani na takarar gwamna da kuma wasu da dama da shugabannin jam’iyyar APC na kasa suka kasa yi.

Daga Fatima Abubakar