TARIHIN ABAYA DA KUMA KASANCEWARTA TUFAFIN KWALLIYA NA MATA.

0
614

Abaya wata doguwar rigace wacce akasari tanada saukin sakawa kuma ana iya sakata akan tufafi yau da kullum,abaya tufafi ne da yake rufe jiki kama daga kafa zuwa hannaye gaba daya haka kuma mafi yawan lokuta abaya baki ne amma wasu lokuta mutum yakanga was launuka iri iri,a yawanci kasashen labarawa ne suka fi yawaita saka abaya amma a yanxu ya zama ruwan dare gama gari a cikin sauran kasashen musulmai na duniya wadda mata suna ganin dacewansa kuma hanya ne mafi sauki wajen rufe jikinsu gaba daya,wasu sun kasance suna hadawa hada nikabi wajen rufe jikinsu gaba daya.haka zalika wadanda ba musulmai bama sun kasance suna saka abaya sabida saukinta da kuma kasancewarta kaya mara nauyi su kan hade da mutanen gari ba ki daya.

Galibi musulunci ta yadda da saka abaya sabida wasu ayoyi da sukazo a alkur’ani mai girma ana amfani da waennan ayoyi don gaskata barin abaya ya zama abin sakawa ga mata.

Daga cikin waennan ayoyi, anyi magana akan amfanin mata su lullaby jikinsu da kyau su boye su ga mazan da basuda alaka dasu musamman idan basa cikin gida .

TARIHIN ABAYA

Abaya bashida tarihin lokacin da aka fara saka shi amma tun lokacin jahilliya akwai sa wato ya kasance fiye da shekaru 4,000.ana amfani dashi ne ta hanyar wayewar yau da kullum, haka zalika a lokacin jahiliyya rufe jikin mace yafi tsanani fiye da addini.

Haka zalika bayan zuwan musulunci da kuma sauke alkur’ani an nunawa mata muhimmanci rufe jikinsu, an nuna cewa yawancin abubuwanda mata wannan lokacin suke amfani dashi wajen rufe jikinsu shine tufafi na abaya na zamanin jahilliya kuma a wannan lokacin ne abaya ta sami ma’ana a addini sai dai kawai yana samun canje canje ne lokacin da kai ke wayewa..

Abaya a wannan qarni a yanxu ya zama gama gari da kuma tufafi da akasani na mata a kasashen larabawa kamansu Qatar da sauran sassan duniyan musulmai na duniya kuma yana daga cikin alamomin tufafi na al’adan larabawa.

ABAYA A SHEKARUN 1970s

A shekarun 1970s abaya ya zama wasu abin gwaje gwaje tare da nau’uka daban daban wadda harda nau’i na silk wadda a rufe kirif yake ko ina na jiki .

 

ABAYA A SHEKARUN 1980s

A wannan shekaran ne aka gabatar da abaya mai kafada wato hannu kuma ta kasance launin baka ce a wannan lokacin da kuma rufe dukkan jiki baki daya,haka zalika a wannan lokacin an fara cikashi da launin ado wadda ya kara kawatashi da kyau.

ABAYA A SHEKARUN 1990s

A wannan lokaci abaya ya kara ingantuwa da kuma samun ci gaba amma salon ta da siffar ta tana nan yanda take ya kasance iri daya teun zamanin da an dai kara samun ado da kuma wasu yaduka tare da karin duwatsu na jikinta wadda ya kara fito da kyanta mata na wasu kasashe suka fara amfani da ita.

ABAYA A SHEKARUN 2000

A cikin shekaru goma na farkon shekarar 2000 gwajin abaya ya dauki sabon ma’ana tareda gabatarda salo iri daban daban da kuma yanka, wasu ana hadasu da wani kala,wasu iya launin baki ne kawai,wasu kuma ana iya musu dinki irin na launin jemage,malam bude ido wato (butter fly ) a turance wani kuma ana mishi fuka fukai tare da yinsu kaloli daban daban,wasu abayanma ana musu nau’i na saka belt masu fadi duka wannan anayinsu ne wajen kara wayewa da kuma ci gaba da ake samu a duniya.

Ayau abaya ya zama tufafi da ya zaga duniya gaba daya wadda har a kasarmu ta Nigeria an dauketa matsayin tufafi na mutunci da kuma kamala domin yadda ya kasance abun rufe jiki ga mata,

Haka zalika masana’antar abaya ta bunkasa sabida yadda abaya ta zama tufafin mata da yafi karbuwa a wajen musulman duniya baki day, a wannan zamani da muke ciki a yanxu abaya yafi karfin abin kwalliya ya zamewa mata tufafi na al’ada wadda a duk ranan jumma’a mata sun kasance suna sakata wajen zuwa masallaci.

Dafatan wannan bayani ya taimaka muku wajen gane cewa abaya tufafi ne da mata ke sanyawa tun shekaru 4000 da suka wuce a duniya.

BY:UMMU KHULTHUM ABDULKADIR