Wasu mutane cikin sauƙin suke fadawa cikin zamba na soyayya, kuma kafin ku sani an yaudare su, an karya masu zuciyarsu ko su ji an yi amfani da su. Duk da haka, kafin duk waɗannan abubuwan su faru, akwai alamun da za su tabbatar da cewa soyayyar karya ce ko kuma ta ganin ido.
- Lokacin da masoyanku ko da yaushe basa iya kallon cikin idanunku. Akwai kowane yiwuwar suna jin cewa su masu laifi ne domin kuwa suna nuna maku soyayyan karya. Duk da haka, wannan kadai ba yana nufin soyayyarsu ta karya ba ce zai iya kasancewa alkunya a soyayya.
- Soyayyar kafofin zumunta da ke kin yin kiran bidiyo. Hasali ma ka nisanci irin wannan soyayyar. A ƙarshe za a yi amfani da ku kuma a yaudare ku.
- Lokacin da yake, son wanni abu ya shiga tsakanin ku tun kafin su san juna sosai. Yana da kyau ku kiyaye irin waennan a soyayya idan ba ku son a cutar da ku ko kuma idan kun damu da zuciyar ku.
- Idan masoyanku suka kasance masu yin maku ihu idan kukayi kuskure, ko kuma suka kasance masu tuna maku kurakuranku na baya, don Allah ku gudu. Bayan rabuwa, irin waɗannan mutanen za su iya amfani da kurakuranku wajan damfaranku, kuma sakamakon ba zai yi kyau ba.
- Lokacin da shi ko ita basa tsoron rasa ku, soyayyar karya ce, haka nan idan za su iya kwana da kwanaki ba tare da sun ji daga gare ku ba, kuma ba su damu ba, ku manta da su ba soyyayan Gaskiya bane.
- Lokacin da ya kasance ko ta kasance ko da yaushe masu karba a soyayya. Toh Babu soyayya ta gaskiya da za ta kasance haka. Mutanen da suke soyayya da gaske suna yin komai don faranta wa abokin zamansu rai.
- Lokacin da mutum ya kasance mayaudari. Hakanan akwai yuwuwar cewa kai ko Ke wani kamu ne kawai. Wasu matan suna yin haka sosai, musamman idan abokin zamansu yana zaune a gari mai nisa, suna amfani da wannan daman, sai su bar ku kuna tsammanin kuna cikin wani soyayya mai mahimmanci.
- Idan suka kwatanta ka da wani… Wanda yake ƙaunarka da gaske, kai ne mafi kyau a gare su bazasu taba hadaku da wasu ba.
- Idan mutum ya aje soyayyanku siri, ba sa son wasu su sani, musamman danginsu Toh Akwai kamshin karya a irin wannan soyayyan.
- Lokacin da ba su son baku lokaci mai kyau.
Daga: Firdausi Musa Dantsoho