YADDA AKE HADA MIYAN KAYAN LAMBU { VEGETABLE SAUCE}

0
1144

Uwar gida  da amarya ku tawo kuji, ba ko da yaushe zaku dinga hada miyan stew ba wasu lokutan a dinga haddawa da miyan kayan lambu wadda a turance ake kiransa da vegetable sauce.

Shi wannan miyan yana da daddin gaske ga saukin hadawa kuma uwargida baya bukatan kashe kudi ga kuma gina jiki.

Kayan lambu na da kyau ga lafiyan jikin dan adam domin yana dauke da sinadirai da ke inganta lafiyan jikin mu, haka zalika, likitoci na yawan bada shawaran a yawaita cin kayan lambu.

ABUBUWAN BUKATA WAJAN HADA WANAN MIYAN SU NE:

*Kaza

*Tumatir

*Albasa mai lawashi

*Karas

*Kabeji

*Dankalin turawa

*Man gyadda

*Jan tattasai

*Koren tattasai

*Gishiri

*Sinadarin daddano

*Thyme

YADDA AKE HADA MIYAN

  1. Ki wanke sai ki yanyanka kayan lambun ki.
  2. Sai ki fere dankalinki ki wanke sai ki yanka shi kananaki markade sh yayyi laushi.
  3. Sai a dauko kazan a yanka, a wanke sai a zuba a cikin tukunya a yanyanka albasa a ciki, a sa sinadarin dandano da thyme, sai a zuba ruwa daidai wanda zai dafa kazan.
  4. Idan da bukata uwar gida zaki iya sa gishiri a tafasan kazan ki. Idan ya dahu sai ki zuba tumatir da kayan lambun ki da man gyadda sai ki rufe ki barshi ya dahu na minti 15.
  5. Sai ki sa karas inki ya dahu na minti biyar.
  6. Bayan minti biyar sai ki zuba nikakke dankalinki da yankakken tattasai da kabeji ki sai ki juya ki rufe ki barshi ya dahu na minti biya.
  7. Toh miyan kayan lambun ki ya hadu, zaki iya cin farar shinkafa ko dafaffen doya ko taliya da wanan miyan.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho