YADDA AKE HADA PAN CAKE

0
208

Pancake ya kasance daya daga cikin kayan  mar mari na girke girke,wadda uwar gida zata iya yinshi a matsayin karyawa,zata iya yiwa yara idan zasu tafi makaranta a saukake ba tare da ta sha wani wahala ba.haka zalika yawancin sindaran da ake amfani dasu wajen yinshi sun kasance abubuwa ne da zasu gina jikin yaro kaman madara,kwai, da dai sauransu.

ABUBUWAN BUKATA SUNE 

Kofi daya na fulawa

Babban cokali biyu na suga

Madara na gari cokali biyu

Babban cokali daya na bakin hoda 

Kwai daya 

Babban cokali biyu na mangyada 

Kofi daya na ruwa 

YADDA AKE HADAWA 

Zaki samu roba naki mai kyau sai ki tankade fulawa naki kofi daya ki zuba sai ki dauko cokali babba ki auna suga sau biyu sai ki saka madara naki shima zaki auna babban cokali guda biyu sai bakin hoda wadda a turance ake kira da “baking powder” shima babban cokali daya, in kin gama hada su a waje daya sai ki samo wata roba naki ki zuba ruwa kofi daya sai ki saka kwai naki a ciki ki kada shi sosai sai ki debo mangyada naki shima cokali biyu ki zuba ki ci gaba da kadawa sai har kinga yayi sosai sai ki dawo inda kika hada fulawa naki sai kina zubawa kina gaurayawa a hankali ba da karfi ba har sai ruwan ya kare,bayan kin gama sai ki kunna gas naki ki daura kaskon suya wato frying pan, sai ki dauko ludayi kina sakawa har sai ya kare zaki soyashi kaman yadda kike soya kwai amma ba shafa mangyada kan kaskon kuma zaki soya gaba da baya har sai kin gama. bayan kin gama zaki iya masa ado da strwaberry ko ki zuba zuma ko nutella akai.

Ana iya cin pancake da zuma ko chocolate na nutella ko zaki iya dan soya kwai a gefe kici dashi.

Rubutawa: UMMU KHULTHUM ABDULKADIR 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here