Da Gangan ‘Yan Fim Suke Janyo Abin Ce-Ce-Ku-Ce Inji Daso

0
350

 Jaruma wadda mabiyanta  a shafin Instagram suka kai miliyan daya, yayin da ba,a  samun jarumai mata masu shekarunta da irin wannan adadi .

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood da ke arewacin Najeriya, Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso, ta ce wani lokacin da gangan ‘yan fim ke tada kura a shafukan yanar gizo wadda zai janyo hankalin jama’a zuwa kansu.

Daso ta bayyana hakan ne a wanni hira na musamman da muryar amurka sukayi da ita.

Ga abun da ta fada kamar  “Kin san mu ‘yan fim kamar ‘yan siyasa muke, idan mun ga dama za mu rikita duniyar gaba daya ido ya dawo kanmu, wato idan mun ji rayuwar ta dan lafa muna so mu motsa ta.” Daso ta ce.

Jarumar wacce ta ke fitowa yawanci a matsayin mai barkwanci, ta bayyana hakan ne a lokacin da akayi mata tambaya kan wani bidiyo da ta wallafa a shafin Instagram inda aka ganta tana wanka a wurin waka na swimming pool.

Daso ta kara da cewa da gangan tayi kuma Sai da ta kaikaici Lahadi babu kowa, ta je ta biya kudi, ta yi wanka ita kadai sai kanwata da ta yi mata  bidiyo.

Ta kuma ce “Alhadulillahi! mabiya miliyan daya da ta samu a Instagram, baiwa ce daga Allah. Kafin ta yi da yawa sun yi, wasu suna da fiye da miliyan daya.”

Ta kara da cewa, “abin da ya sa abin ya zama babba a idon jama’a, shi ne, saboda ganin ita dattijuwa ce kuma matar aure, shi ya sa ake cewa ya aka yi haka?

Fim na baya-bayan nan da jarumar take taka rawa a ciki shi ne, fim din “Gidan Danja,” wanda fim ne mai dogon zango.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho