YADDA AKE HADA YOGHURT SALAD

0
740

Shi wannan salad in na daban ne ba irin waenda kuka saba gani bane, ana hadda wannan salad in ne da yoghurt da kuma iyayan itatuwa, kuma yana da saukin hadawa baya daukan fiye da minti goma sha biyar wajan hadda shi.

Wannan salad in yana da daddi kuma ya na da kosarwa.

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

  • Yoghurt
  • Strawberries
  • Seedless Grapes
  • Ayaba
  • Tufa
  • kwakwa
  • Condensed milk

YADDA AKE HADAWA

  1. Zamu farad a wanke iyayan itatuwan mu tas.
  2. Sai mu yanyanka ayaba, tufa da strawberries inmu kanana.
  3. Shi graphes in tunda seedless ne zamu barsh a kwaya kwayansa, sai mu kankare kwakwa watto grating kenan.             
  4. Zamu samu kwanu mu na salad watto salad bowl,mu zuba yankaken iyaya itacen mu a ciki.
  5. Sa’annan mu zuba yoghurt in mu a kai mu gauraya.           
  6. Idan ya hade gabaki daya sai mu zuba condense milk mu juya.
  7. A sa a fridge yayyi sanyi sai a sha lafiya.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho