Hadaddiyar hanyar hada salak in Najeriya na gargajiya salad mai daddi. Salak na da launi mai kyau, yana cike da abubuwan gina jiki, yana da kosarwa sosai kuma yana da daɗi . ana iya cin salak ta hanya daban daban ana iya cinsa a matsayin appetizer, ko azaman babban abinci mai daɗin gaske kuma yana da sauƙin hadawa. A zahiri salak abinci ne da ke tafiya a kowani lokaci.
Kuyi la’akari da cewa kayan lambun ba dole ba ne su kasance masu ganye don cancantar kasancewa cikin salak. Wannan Salak mai dadi ya kunshi kayan lambu danye da dafaffe, taliya, Kwai da sauransu. Tare da duk waɗannan sinadaran, tabbas wannan Salak akansa abinci ne mai daɗi amma kuma ana iya haɗa shi da shinkafar Jollof, Fried rice, Soyayyen kaza da sauransu.
Abubuwan mafi muhimmanci da ake amfani da su wajan hada salak sune Letus da Kabeji amma suna kewaye da Tumatir, taliya, Kwai, Cucumber, Wake da masaran gwangwani. Duk waɗannan sinadarai suna sa wannan salak in ya zama ya kayatu don nishadantar da jama’a kuma kamar tare da yawancin salads, yana da sauƙi. Misali, ana iya amfani da dankalin turawa a madadin taliya.
Abubuwan bukata wajan hada salak
* Karas 2
*Kofuna 2 na yankakken letas
*Kofuna 2 na yankakken Kabeji
*Tumatir biyu mai kwari
*Kofi 1 na taliya ko dafaffen dankali
* Dafaffen Kwai Manyan 2
*Cucumber Matsakaicin Girman guda 1
*Waken Gwangwani
*Masarar gwangwani
*Babbar cokali 8 na Heinz Salad Cream
Yadda ake hadda salak
- Ki shirya kayan lambun ki duka sai ki wanke su sosai cikin Ruwa mai gudana.
- A dafa kwai a kuma tafasa Taliya da gishiri kadan har sai ya dahu.
- Sai ki yanka kabejinki da latas, ki yanka tumatur din ki yanka kananan, kina iya gursa karas dinki ko ki yanka su kananan ki kuma yanka Cucumber inki
- Sai ki zuba komai a cikin kwano mai tsafta banda kwai da Cream sai ki rufe shi da roba ko murfi mai matsewa sai a saka a cikin firiji na akalla awa 1.
- Bayan awa daya sai a cire shi daga Firji lokacin da aka shirye yin amfani dashi, sai a chakuda su tare a sa ƙwai da aka dafa akan salak in. Sa a hada tare da cream in salak na Heinz .
- A ci lafiya.
By:Firdausi Musa Dantsoho