Gashi wani tushen kwalliya ne da yake da muhimmanci ga mata kuma ya zama wajibi mata su kula dashi, domin kuwa a duk lokacin da mace take so taga ta burge mijinta toh sai ta hada da jawo hankalishi da gashi mai kyalli da kuma tsayi.
Haka zalika wasu Matan da dama sun kasance suna son ganin kansu da gashi mai tsayi kamar na Indiya. Gashi na daya daga cikin ababen da ke kara wa mace kyau, don haka ya kamata mu kula da gashinmu sosai.
Wannan hadin da na kawo muku yana kara wa gashi maiko, wajen hana shi karyewa da sanya shi tsayi da laushi.
Wannan hadin akan yi shi ne kamar sau biyu a wata. Idan mutum ya kasance mai yin wani hadi ne daban wanda ba wannan ba, bai kamata a rika hada wannan gyaran gashin da wani daban ba in ba haka ba, kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba.
ABUBUWAN DA ZAA BUKATA SUN HADA DA:
- MAN KADANYA.
- MAN KWAKWA
- RUWAN DUMI
- MAN ALAIYYADI
Da farko sirri na farko da zan iya bude muku shi ne uwar gida ki kasance a koda yaushe gashinki a rufe yake, walau da dankwali ko kuma hula domin kuwa shi gashi a koda yaushe yana son dumi ne, a lokacin da kike barinshi iska na shiga yana sabon gashi tsirowa haka kuma yana saka wanda ya tsiro din karyewa da haka ne zakiga dan wanda kika tara din duk ya kade. Don haka ya zamana cewa kullum gashinki a rufe yake shiyasa zaku ga yawanci duk masu amfani da wani gashi bayan gashinsu sunada gashin sosai, ba wani abu bane illa wannan Karin da sukeyiwa gashin yana rufe asalin nasu sai ya kasance cikin dumi.
Haka zalika ya kasance kin kwaba man gashinki tareda hada man kadanya, man kwakwa da kuma man alaiyaddi, domin dukkaninsu sunada wani sinadari dake kara tsiro da gashi mai laushi.
Haka zalika ya zamana kina steaming wato turara gashi ko sau daya ne a wata domin Kaman yadda na fada muku shi gashi dumi yakeso. Haka kuma bayi idan nace bayi ina nufin kina fesa mishi ruwa kullum kullum kuma idan har kikayi wannan bayin ki tabbatar da cewa baki saka mishi hand dryer ba ki barshi da kanshi ya bushe. Alla yasa a dace.
UMMU KHULTHUM ABDULKADIR