Bai kamata ku tsaftace kunnuwanku kwata -kwata ba, kuma musamman ba tare da auduga cotton bud ba.
Dattin Kunnen yana da amfani kuma yakamata jikinku ya kawar da dattin kuni idan yayyi yawa ba tare da sa hannun ku ba.
Dokta Lee ya yi bayani: “Earwax hade ne na sebum – wani abu mai maiko da aka samo daga sinadarin sebaceous a cikin fata wanda ke rufe ramin kunne – da matattun sel fata wadanda ke ratsawa a wannan yankin.
“Dattin kunne yana da amfani saboda, tare da gashi da ke cikin kunne, yana taimakawa hana ƙwayoyin cuta kamar bakteriya da ƙwayoyin cutan virus shiga cikin kunnen da haifar da cutar kunni.
“Dattin kunne a zahiri yana zubowa daga kunnuwan ku ba tare da kun sani ba.
“Yayyin da kuke magana, ku ci ko kuma tauna abu, tsokokin kumatunku suna tausa hankali , kuma a ƙarshe Dattin kunin ya faɗi da sauƙi.
” ƙaramin adadin dattin na fadowa ne lokacin da muke wanka.”
By: Firdausi Musa Dantsoho