YADDA ZAMU GYARA FATANMU DA KANKANA

0
327

Kankana na daya daga cikin yayan itatuwa da ke dauke da sinadaren gyaran jiki da gautsin fata da kuma ragetsufar jiki, domin kuwa tana dauke da sinadaren dake wanke maikon dake taruwa a magudanar gumi a fata, wanda yawanci shi ke haifar da fesowar kuraje da dama a jikin mutum.

Akwai hanyoyi da dama da zaku iya bi wajen amfani da kankana domin hana kurajen fata da kuma samun fata mai laushi da kuma sheki a koda yaushe, wanda a maudu’inmu na yau na kawo muku shi.

 

  1. Abu na farko shine ga masu matsalan kurajen fuska: A samu kwallon kankana a busar a rana sannan a daka yayi laushi sannan a tafasa ruwa sai a zuba sai a tace sannan a rika wanke fuska dashi.
  2. Abu na biyu shi ne ga masu matsalar yankwanewar fata: A markada kankana sannan a zuba mata zuma kadan sai a rika shafawa a inda fatar ke yankwanewa sau biyu a ranan, idan kuma hakan bai biya bukata ba sai a hada kankana da ruwan lemun tsami sai asa sukari a gaurayasu guri guda sai bayan sukarin ya narke sai a rika shafawa fuska musamman daidai inda fatar ta yankwane.
  3. Abu na uku shi ne ga masu matsalar kodewar fuska: za’a markada kankana tareda kukumba sai a rika shafawa kamar sau biyu a rana, wannan hadi yana matukar magance matsalar kodewar fuska. Haka kuma zaa iya markada kankanan zalla sai a dauko auduga a na shafa ruwan a fuska a barshi yayi tsawon minti goma kafun a wanke.
  4. Abu na hudu shine ga masu matsalar gautsin fata: a markada kankana sannan a zuba mata man ridi dana kwakwa sai a shafe a fata a barshi ya kai tsawon mintuna ashirin sannan a wanke shi.
  5. Abu na biyar ga masu matsalan kyasbi: A samu ya’yan kankana a nika shi bayan ya bushe a kwaba da zuma ana shafawa sau biyu a rana.

UMMU KHULHUM ABDULKADIR