Yan bindiga sun kai hari a wani shingen rundunar sojoji da ke kusa da Zuma Rock.

0
165

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari a wani shingen binciken sojoji da ke kusa da Zuma Rock da ke kan iyaka tsakanin jihar Neja da babban birnin tarayya Abuja a yammacin ranar Alhamis.

Har yanzu ba a kayyade bayanai kan harin da aka kai har zuwa lokacin da ake cika wannan rahoto.

Sai dai an tattaro cewa jami’an rundunar sojin Najeriya sun fara aikin share fage bayan harin.

Lamarin da aka ce ya haifar da kulle-kulle a yankin.

An kuma tattaro cewa sojojin Najeriya sun tare hanyar Mandala zuwa Kaduna.

A wata majiyar soja wanda ya nemi a sakaya sunanta ya ce, “’yan ta’addan sun kwashe sama da mintuna 30 suna iko da yankin inda suka yi ta harbe-harbe kafin su nufi hanyar Kaduna ta hanyar mota.”

Sai dai sojoji daga barikin Zuma sun mamaye wurin da lamarin ya faru tare da kwace iko.

Ya kuma tabbatar da cewa, daga baya tawagar ‘yan sandan da ke sintiri ta isa wurin.

Kokarin samun Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, bai yi nasara ba.

Shi ma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi, bai amsa kiran da wakilinmu ya yi masa ba.

 

Daga Fatima Abubakar