Yan bindiga sun kashe wani mutum a Gana street da ke Maitama a daren jiya laraba.

0
29

Akalla wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun harbe mutum daya har lahira da misalin karfe 8:45 na daren ranar Laraba a titin Gana da ke unguwar Maitama a babban birnin tarayya Abuja, yayin da wani kuma aka yi awon gaba da shi.

Wasu mazauna unguwar da suka zanta da wakilinmu bisa sharadin sakaya sunansu, sun ce an kashe wanda aka kashe ne a lokacin da yake kokarin kubutar da wani mutum da ‘yan bindigar suka tilastawa shiga wata bakar mota kirar Prado SUV.

Majiyar ta ci gaba da cewa, motar SUV din tana nan ne a kan titin Gana, inda daya daga cikin ‘yan bindigar ya harbe shi a kai, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa nan take.

An tattaro cewa wadanda ake zargin sun tsere tare da wanda suka tilastawa shiga motar ta su yayin da gawar marigayin ke kan titi cikin dare.

Wasu majiyoyi sun yi zargin samari ne da suka rika yawo a yankin, inda suka kara da cewa a ‘yan kwanakin nan, manyan kantuna da shagunan sayar da magunguna da ke Maitama sun zama abin kai hari. Hakan dai ya faru ne yayin da mazauna yankin suka yi zargin cewa ‘yan sanda sun yi watsi da yankin duk da koke-koke.

Da take tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, mai magana da yawun ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta yi ikirarin cewa ‘yan sandan na gudanar da bincike a kan lamarin, yayin da ta musanta zargin yin watsi da su.

A cewar ta“Muna gudanar da bincike kan lamarin, amma ba gaskiya ba ne na cewan  ‘yan sanda ba su yi wani abu ba wajen tabbatar da sa ido kan shagunan sayar da magunguna a yankin, kamar yadda ake zargi. Kwamishinan ‘yan sanda, Babaji Sunday, yana aiki ba dare ba rana don ganin an samu tsaro a babban birnin tarayya Abuja, kuma kowa ya ci gaba da gudanar da sana’arsa cikin lumana.

Ta ce, “Al’amarin satar mota ne. Watakila ‘yan fashi da makami sun gano mutumin zuwa wajen da ya sayi motar. Sun yi kokarin kwace masa mota, ana cikin haka ne aka  harbe mutumin. Daga baya aka garzaya da shi asibiti, amma abin takaici ya rasu.

“An gano mutumin da aka sace, kuma yana samun sauki yanzu. ‘Yan sanda suna tare da shi a daren jiya kuma muna yin iya bakin kokarinmu wajen bin diddigin motar domin mun yi imanin cewa ba za su amfana da su ba, kuma babu shakka motar za ta tsaya a wani wuri.”

 

Daga Fatima Abubakar