Yan bindiga sun yi garkuwa da ciyaman na Keffi ta jahar Nasarawa Hon.Muhammad Baba Shehu tare da kashe dan sanda daya.

0
62

Rahotanni sun ce an sace shugaban karamar hukumar Keffi ta jihar Nasarawa, Muhammad Shehu tare da direban sa, wadanda har yanzu ba a tantance ko su wanene ba.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu cewa, shugaban a ranar Juma’a da daddare, yana tafiya tare da direbansa da ‘yan sanda cikin tsari amma ‘yan bindigar sun tare shingayen titin Keffi zuwa Akwanga inda suka yi ta harbe-harbe  wanda hakan ya tilasta musu tsayar da motar su kafin su kai farmaki aka yi garkuwa da su.

Majiyar ta ci gaba da cewa, a kokarin ganin an shawo kan lamarin, dan sanda ya yi kokarin dakile harin amma abin takaici ya rasa ransa.

“Mun samu labarin cewa Shugaban Hukumar ya fito ne daga wani shiri da kungiyar Old Boys Association ta Keffi ta shirya a Kwalejin Gwamnati da ke Keffi lokacin da aka kai wa motar sa hari.

“’Yan sandan sa bisa tsari sun yi kokarin shawo kan lamarin amma ‘yan bindigar sun harbe shi har lahira yayin da su ka yi garkuwa da shugaban da direbansa,” inji majiyar.

Da yake tabbatar da harin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Adesina Soyemi, ya ce jami’an ‘yan sanda sun shiga aiki gadan-gadan a inda aka kai harin domin kubutar da wadanda abin ya shafa tare da kamo masu garkuwa da mutane.“Yanzu haka jami’an ‘yan sanda suna yankin da aka yi garkuwar da su.

Adesina ya kara da cewa, Mun karbe muhalli kuma ina tabbatar muku nan ba da jimawa ba za a kubutar da su kuma wadanda suka aikata wannan aika aika ba za su tsira daga fushin doka ba,”

Daga Fatima Abubakar.