Yana da babban hazaka – Jay-Jay Okocha ya bayyana dan wasan da yake so

0
56

Fitaccen dan wasan Najeriya, Austin Jay-Jay Okocha ya zabi Jude Bellingham na Borussia Dortmund a matsayin dan wasan da yake matukar so a gasar ta Jamus.

Okocha ya ce Bellingham yana da hazaka sosai, ya kara da cewa zai yi kyau Dortmund ta rike shi muddin za su iya.

Lokacin da aka tambaye shi yayi hasashen wani matashin dan wasa wanda zai iya jin dadin kakar wasa a Bundesliga, Okocha ya yi sauri ya ambaci sunan dan wasan na Ingila.

“Ina son Jude Bellingham, ya nuna cewa yana da babban hazaka. Ya yi wasa mai kyau a kakar wasan da ta wuce kuma ina sa ran zai ci gaba daga inda ya tsaya. Hakan ya nuna yadda Dortmund ta kimanta shi, dan wasa ne da nake matukar so, “in ji Okocha kamar yadda Sportskeeda ta ruwaito.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho