Za Mu Sake Binciken Baddakalar Bidiyon Dalar Ganduje – Muhuyi Ya Sha Alwashi

0
38

Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Barista Muhuyi Magajin Rimin-Gado, ya sha alwashin sake bude binciken da ake yi wa tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan faifan bidiyon daloli.

Idan dai ba a manta ba, wata kafar yada labarai ta yanar gizo, Daily Nigerian, ta fitar da wasu faifan bidiyo na Ganduje da ake zargin yana karbar kudade daga hannun ‘yan kwangila har dala miliyan 5.

Duk da cewa tsohon gwamnan ya musanta zargin, yana mai cewa faifan bidiyon an hada shine.

Sai dai da yake magana a gidan Talabijin na Trust TV, Rimin-Gado, wanda Ganduje ya tsige shi bayan yunkurin binciken tsohon iyalan gidan gwamnatin jihar bisa zargin almubazzaranci da kudade, amma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da shi bakin aikinsa, bisa bin umarnin kotu, ya ce binciken ya zama dole.

Rimin-Gado da yake tunawa da abin da ya fada kan bidiyon dala a wata hira da aka yi da shi, ya ce, “Ina nufin duk wata magana da na fada lokacin da nake kan mulki. Mun bude bincike amma akwai wasu iyakoki a lokacin domin shi ne gwamna mai ci.

“Kowane gwamna mai ci, mataimakin gwamna ko shugaban kasa yana da kariya. Yanzu wannan iyaka babu ita. Hukumar za ta yi abin da ya dace.”

Ya kuma yi magana kan batutuwa da dama, inda ya musanta cewa an yi amfani da shi wajen tsige Alhaji Muhammadu Sanusi daga matsayin sarki.

Ya kuma kare wasu manufofin gwamna mai ci.

Firdausi Musa Dantsoho