Dan wasan Ghana Gyan ya yi ritaya daga kwallon kafa

0
17

Dan wasan Ghana Asamoah Gyan wanda mai rike da tarihin zira kwallaye fiye da kowa  ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa.

Dan wasan mai shekaru 37 yayin da yake sanar da matakin daya dauka na yin bankwana da tamaula, ya danne zuciyarsa a daidai lokacin hawaye ke fitowa daga idanuwansa a kan mambari tare da tsohon dan wasan Ivory Coast Didier Drogba a babban birnin Ghana, Accra.

“Lokaci ya yi da za a gaya wa kowa. Lokaci ne mai matukar wahala, ”in ji tsohon dan wasan wanda ya ci wa kasarsa kwallaye 51 a wasanni 109.

Daga baya Gyan ya shiga shafukan sada zumunta inda ya bayyana dalilin da ya sa yake kiran lokaci a kan aikinsa na shekaru 20.

“Lokaci ya yi,” in ji shi, “in rataye riga da takalman kwallona a cikin daukaka yayin da na yi ritaya a hukumance daga wasan kwallon kafa.

“Matakin da ke da wahala ga kowane ɗan wasan ƙwallon ƙafa, lokaci ne da duk ‘yan wasan ƙwallon ƙafa ba sa fata amma idan lokacin yayyi dole a dakata.”

Gwarzon dan kwallon Afrika na BBC na shekara ta 2010 ya fara buga wasansa na farko a duniya a shekarar 2003 yana dan shekara 17, inda ya maye gurbinsa a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Somalia. Ya yi bayyanarsa ta ƙarshe a Black Stars a cikin 2019.

Ya buga wasanni bakwai na gasar cin kofin Afrika, inda ya taimakawa Ghana ta zo na uku a shekarar 2008 sannan kuma ta zo ta biyu a 2010 da 2015.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Afirka ta bayyana shi a matsayin “cikakkiyar gwarzo na wasan” da “daya daga cikin mafi kyawun da aka taba yi”.

Firdausi Musa Dantsoho