Zamfara: An sako masu ibada 43 da aka sace

0
111

Akalla masu ibada arba’in da uku da aka sace a jihar Zamfara, sun samu ‘yancinsu.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyar bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a tsakiyar masallacin garin Zugu da ke karamar hukumar Bukkuyum.

Rahotanni sun ce an kashe wani mai suna Babangida Muhammadu (23) kafin a sako wasu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammed Shehu, ya tabbatar da sakin mutanen.

Sai dai ya musanta sanin duk wani lamari da aka ruwaito wadda ya shafi wanda aka kashe. Ya ce, “Rundunar ta na sane da cewa an sako duk wadanda akayi garkuwa da, amma ban san an kashe wani ba ko kuma an biya kudin fansa.” Shehu ya bayyana cewa rundunar tana kokarin tabbatar da tsaron jihar, ciki har da wuraren ibada. Ya ce lamarin a Zugu ya faru ne saboda wani yanki ne da ke wajen jihar da mutane ba su da yawa. A halin yanzu, ya koka da cewa babban batun da aka ci karo da shi a jihar shi ne na masu ba da bayanan tsaro ga maharan.

 By: Firdausi Musa Dantsoho