corset, wani tufafi ne da ake sawa don gyara siffa ko takura kugu da goyan bayan ƙirjin, wadda ya kasance a matsayin tufafi tun daga tushe na zamanin kayan ado na waje. A lokacin farkon zamanin corsetry, abun ado da ake kira da corsets ya fara ne kafin karni na 19 wanda yake tare da gyara kasusuwan mace -ya gyaggyara saman jikin mace zuwa siffar V kuma ya baje tare da tura ƙirjin. Wasu an haɗa su da riguna ko za a iya ɗaure su da su domin a adana siffa mai faɗi a kugu.Daga baya, da kwalliya ya kara wanzuwa an canza sa zuwa zuwa abun ado mafi kyau ga mata.
Haka zalika a wannan zamanin corset ya kasance abu mafi muhimmanci da mata suke Amfani dashi wajen kawata kwalliyansu musamman a lokacin bukukuwa.
A wannan Makala namu na yau na kawo muku hanyoyin da zakubi wajen amfani da kwalliyan corset musamman ga amare.
Na farko da kuma mafi mahimmancin shine ki nemo corset wanda ya dace da nau’in jikin ki kuma zai dace da shi daidai. Wasu sukanyi amfani dashi a bayyane, wasu kuma ana musu amfani dashi a sirrance wadda shi ne abu mafi kyau musamman a al’adanmu na arewa. Haka zalika akwai na’uka na corset wadda sai kin kula sosai kafun ki cire mai kyau.
Abu na biyu shi ne idan kika samu nasarar samun corset mai dacewa, to, zai iya ba da cikakken goyon baya ga jikinki, wanda zai taimake ki kula da daidaitattuwanki. Hakanan corset zai taimaka muki don inganta yanayin tsarin jikinki.Saboda waÉ—annan dalilai, samun corset mai dacewa yana da mahimmanci. Don haka, ki tabbatar da sanin siffar jikin ki kuma ki tuntuÉ“i masana don sanin nau’in corset wanda zai iya taimakawa masu lanÆ™wasa daidai.
Daga karshe kuma ki tabbatar da cewa kayan da zakiyi dinkin a jiki kayane na biki ba wain a zaman gida ba, domin kuwa kwalliyar corset yafi dacewa da kayan zuwa wani taro ko kuma event.
UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.
Â
Â