Lalle kamar yadda aka sani na daga cikin kayan kwalliyar da mata ke amfani da su musamman a lokacin taron bukukuwa ko suna, a wasu lokutan mata na amfani da shi don kara kyau ko kwalliya ta barge abokin zama wato miji ko saurayi.
Amfanin lalle a kasar Hausa ya zama tamkar al’ada a lokutan bukukuwan addini da na al’ada kamar su Sallah Karama da Babba, Aure, Taro, da sauransu.
Ana yin lalle ko kunshi a Hausan ce a kuma zamanin nan don kaita kwalliyar yau da kullum da kuma na gargajiya ne ama zamanin yanzu ya sa ana iya yin zane kala-kala ko kuma a bar shi a jaa ko kuma a bar shi ya yi baki, hakan ya danganci mai mace ta ke so.
Safrat Gani