‘Yan Bindiga Sun Sace Alƙalin Babbar Kotun Kebbi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza

0
6

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza, bayan sun kai hari gidansa da ke garin Bunza a daren Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare, jim kaɗan bayan Mai Shari’ar ya dawo gida daga wata tafiya da ya yi zuwa Jihar Sokoto.

Shaidu sun ce maharan sun kutsa cikin gidan tare da yin awon gaba da alkalin zuwa wani wuri da ba a sani ba. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana ko sun tuntubi iyalansa ko kuma sun nemi kuɗin fansa ba.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an tsaro sun fara bincike tare da ƙaddamar da wani samame domin ceto Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza da kuma kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Lamarin ya jefa al’ummar garin Bunza da ma daukacin Jihar Kebbi cikin fargaba, yayin da ake kira ga jami’an tsaro su gaggauta ɗaukar matakan da za su tabbatar da kubutar da alkalin cikin ƙoshin lafiya tare da hukunta masu hannu a wannan aika-aika

 

Hafsat Ibrahim