ABIN DA YA SA MATA SUKA TSANI AYI MUSU KISHIYA

0
353
Kishi wata halitta ce da Allahu ya yi ya kuma dasa shi a zuciyar ko wani dan Adam a zuciya. Babu wanda baida kishi, kuma babu wanda ke son ganin wani ya rabi abinda yakeso,ko yaga anyi masa kishiya.
Ga mata kuma, akace kishi shi ne kumallon su, abin haka yake, saboda dik inda aka shiga aka fita, anfi tunanin mata sun fi kowa nuna kishinsu a fili.
Za a iya cewa hakan na faruwa ne saboda addini bawa namiji damar auren mace fiye da daya.
Wasu matan suna iya boye kishin su, wasu kuma basu iya wa,shiyasa da zaran wasu matan sunyi aure,hankalin su baya kwanciya, a kullum cikin fargaba suke akan randa miji zai kawo masu zancen karin aure .
Kullum saka masa ido take da binciken wayar sa taga ko yana soyayya da wata daban. 
Akwai dalilai da dama da ke saka mace ta ji ta tsani kishiya.
Nafarko, zai iya yiwuwa mace ta taba fuskantar yadda zama yake da kishiya a gidansu, watau babanta ya taba auren mace fiye da daya kuma abun bai yi dadi ko armashi ba, toh inhar tayi aure, zata rika jin fargaba kar abinda ya faru a gidansu ya dawo yana faruwa a nata gidan.
Sai kuma wasu matan Saboda zallan madaran kishi ne yayi masu yawa, in suna tare da abu,basu kaunar ganin wani abu ya rabe shi,,wata mace bata ko kaunar ganin mijinta ya kalli ko ‘yar uwarsa ce,nan da nan kishin ta zai motsa taji duniyar na juya mata, irin wannan kishin ne ake neman tsari da shi.
Wasu mata da dama kuma suka ce ba kishiya bace ake gudunta, a a, me zata zo dashi.
Mace ce zata zauna tare da mijinta shekara da shekaru cikin kwanciyar hankali, amman da zaran yakara aure zata nemi kwanciyar hankalin nan ta rasa, wata zata shigo ta nemi hanyar raba ta dashi da kuma yaranta. Wasu marasa imanin ma,har zuwa wajajen ‘yan tsubbu suke domin salwantar da rayuwar kishiyar. Wannan na daya daga cikin manyan abun da yasa mace ke tsoron kishiya.
Wata kuma mijinta na kyauta ta mata sosai, ba bu abinda ta nema ta rasa ,toh in yazo mata da zancen zai kara aure, zai yi wahala ta yarda,domin tana ganin in har ya karo auren,zai iya rage kyautata mata da yaran ta da ya saba yi. Ire iren wannan tunanin na saka mace taji ta tsani kishiya kuma bata son ayi mata.
Abinda ke faruwa yawanci shi ne yadda maza ke son karin aure ko da basu da ikon yi, ma’ana ,namiji bashi da kudin karin aure,kuma babu inda zai ajiye matarsa, amman haka zai daddage ya karo wata matan, wasu lokutan ma,yana iya tashin yara a dakin su ya saka amaryar a ciki,yaransa kuma su rika bin daki daki suna kwana. Hakan na janyo matsi ga uwargida, da jin ta tsani karin auren da zaiyi. A yawancin lokuta, wasu mazan na kara aure ba tare da isashen abinda zasu kula da iyalan su dashi ba. Hakan na sa wa abarwa mace nauyin kula da kanta da yaranta. Wanda hakan bai dace ba.
Duk da wannan, yakamata mace tayi kokarin kauda kai da danne zuciya idan har mijinta ya kawo mata zance karin aure, saboda Allah ya lamunce ma maza su auro fiye da daya idan suna da hali.
Dole ne mace ta yi hakuri da wannan kuma ta rungumi kaddara, ta kwantar da hankalinta ta mika lamuranta zuwa ga Allah, idan tayi hakan,sai Allah ya kawo mata dauki.
Daga Maryam Idris