Babban Bankin Najeriya ta sanar da cewa zata canja zuwa anfani da sabbin kudi daga 15 ga watan Disamba.

0
84

Shugaban Babban Bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, a yau Laraba, ya bayyana cewa, ana shirin kaddamar da sabbin takardun kudi na Naira nan da ranar 15 ga watan Disamba na wannan shekara, inda ya nemi masu ajiya da su shiga bankunan domin musanya tsofaffin kudaden su da sababbi kafin 31 ga  watan Janairu 2023.

Emefiele ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na musamman da aka yi a Abuja, inda ya ce matakin ya samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce canjin dai zai shafi takardar naira 1000,500 da kuma naira 200.

Daga Fatima Abubakar.