Allah yayiwa jarumin kannywood Ahmed tage rasuwa.

0
499

Allah yayiwa daya daga cikin fitaccen jarumi mai daukar hoto (camera man) na masana’antar kannywood malam Ahmad Aliyu tage rasuwa, tage ya rasu ne a jiya ranar litinin 13 ga watan satumba shekara ta 2021 a asbitin nasarawa dake jihar kano.

mun samu labari daga mujallar fim kan cewa tage ya rasu ne sanadiyyan matsalar bugun zuciya, tage ya rasu yanada kimanin shekaru 55 a duniya, ya kuma bar ‘ya’ya 21 da mata biyu.

Tage ya kasance jarumi ne a kannywood wanda yafi fitowa a fina-finai na wasan barkwanci, ya fara a matsayin daukan hoto daga baya ya dawo jarumi a masana’antar

Jarumai da dama sun tura a shafukansu na yanar gizo tare da alhini na mutuwar dan uwansu.

Dinbin mutane tare da jaruman kannywood sun halarci jana’izarsa wadda suka hada da Alhassan kwalle,shu’aibu idris lilisco,Hassan giggs,Abba almustapha, sunusi Oscar da sauran ransu, tare da masa addu’a a shafukansu na yanar gizo.

 

Allah yaji kan Ahamd tage ya masa rahama.

Ameen..

BY:UMMU KHULTHUM ABDULKADIR