Dangote Ya Ba Da Aikin Yi Ga Daliban Da Suka Kammala Karatu a Jami’ar Jihar Kano

0
24

Shugaban kamfanin Dangote Aliko Dangote ya yi alkawarin samar da aikin yi ga dukkan daliban da suka kammala digiri na farko a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano da ke Wudil.

 

 An canza sunan makarantar zuwa ga sunan wanda ya fi kowa kudi a Afirka.

Rahotanni da dama sun bayyana cewa Mataimakin Shugaban Jami’an Farfesa Shehu Musa ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Kano yayin wani taron tattaunawa da ‘yan jarida kan sauya sunan jami’ar zuwa sunan Shugaban Jami’ar, Aliko Dangote.

Mataimakin shugaban jami’ar ya ce Dangote ya yi alkawarin samar da aikin yi ga daukacin daliban jami’ar da suka kammala digiri na farko da na biyu a jami’ar.

 

 Ya kara da cewa, wanda ya fi kowa kudi a Afirka, tuni ya bukaci mahukuntan jami’ar da su ba shi jerin sunayen duk wadanda suka kammala karatun digiri na farko a jami’ar domin samun aikin yi ta nan take.

 

 Ya ce Dangote, shugaban jami’ar, ya kuma gina dakunan kwanan dalibai guda biyu da kowannensu dakuna 500 ga daliban jami’ar mata.

Mataimakin shugaban jami’ar ya ce baya ga gudunmawar da ya baiwa jami’ar, shugaban kamfanin Dangote ya yi alkawarin daukar malaman jami’o’in kasar waje tare da gina musu masauki.

 

 Tuni dai an yi hira da malamai 15 kuma suna jiran amincewar shugaban jami’ar na karshe.

 

 Musa ya bayyana sauya sunan jami’ar da sunan Dangote a matsayin wanda ya dace kuma abu ne mai kyau a yi.

 

 Ya bukaci masu hannu da shuni a Najeriya da su dauki hankalin Dangote su zuba jari a jarin dan Adam da ilimi domin amfanin kasa.

Ya godewa Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano, majalisar zartarwa ta jihar da gwamnatin jihar Kano bisa ci gaban da suke baiwa jami’ar.

Daga : Firdausi Musa Dantsoho