Amfanin bawon ayaba a jikin mu

0
145

1.Farin hakora:
Shafa bawon ayaba kullum tsawon mako guda akan hakora na kamar minti daya.  Wannan hakika yana haifar da fararen hakora, wanda za’a iya kashe kuɗi da yawa akai.
2. Yana kawar da Warts:
Bawon ayaba na taimakawa wajen kawar da warts da kuma kawar da faruwar sabobin fitowa.  Don yin haka, kawai a shafa bawon a wurin da abin ya shafa ko kuma a ɗaure bawon a  wurin cikin dare.  Wannan yana daya daga cikin mafi sauki hanyoyin amfani da bawon ayaba ga fata.
3. Yana maganin Pimples:
Kawai tausa bawon ayaba a fuska da jikinka na tsawon mintuna 5 a kowace rana don magance kurajen fuska.  Ya kamata a ga sakamakon a cikin mako guda.  A ci gaba da shafa bawon har sai kurajen su bace.
4. Yana Rage tamoji (Wrinkles):
Bawon ayaba yana taimakawa wajen sa fatar jikinku ta sami ruwa.  Ƙara gwaiduwa kwai a cikin bawon ayaba da aka daka.  Ki shafa wannan hadin a fuskarki ki barshi na tsawon mintuna 5.  A wanke bayan minti 5
5. Yana rage layukan shekaru masu kyau:
Bawon ayaba idan aka shafa a fuska yana sa fuska laushi da kuma tsantsin fata yana rage layukan jiki da kuraje.

Daga Faiza A.gabdo