A sanadiyar mutuwar Ifeanyi, Davido ya auri budurwar sa Chioma a sirrance.

0
48

.Davido da Chioma  sun sha wahala tare da bakin ciki sakamakon rashin dansu, Ifeanyi Adeleke.

Gistlovers blog ya yi zargin cewa mawakin ya auri Chioma a asirce bayan mutuwar dansu.

Bikin aure na gargajiya wanda aka yi a gidan mahaifinsa tare da abokai kaɗan da yan uwa da suka halarta ba tare da izinin kyamara ba.

A cewar shafin, an biya kudin sadakin amaryar Chioma gaba daya.

Ku tuna cewa Davido ya sha alwashin auren Chioma a shekara mai zuwa, amma bayan da lamarin ya faru, mawakin ya gaggauta aurenta.

An yi bikin auren gargajiya ne a ranar 6 ga Nuwamba, domin tabbatar wa Chioma matsayinta a zuciyar sa.

An kima tattaro cewa Rijistar su na zuwa wani lokaci a mako mai zuwa, kodayake; har yanzu ma’auratan suna cikin jimamin rashin dansu.

Bikin Mara Ƙarshe kamar yadda Davido Ya Tabbatar da Shirin Auren Chioma a 2023.

Davido da chioma sun sake farfado da soyayyar su a sarari a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata bayan da suka samu matsala shekarar 2019. Sai dai alakar tasu ta yi tsami bayan haihuwar dansu, Ifeanyi.

Daga alamu na baya-bayan nan, da alama Davido zai daura aure a karshe tare da Chioma Rowland bayan shekaru masu yawa da dangantaka.

Tauraron mawakin ya fadi hakan ne a lokacin da yake tafiye-tafiye a Landan, a ziyarar da ya kai wa shahararren limamin coci, Fasto Tobi Adegboyega.

Daga faifan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, an ga Fasto Adegboyega yana rungume da Chioma yana cewa “matarmu, matar mu ta gaske” kuma Davido ya mayar da martani da cewa “kashi dari bisa dari, ya fadi kasa a 2023” wanda ke nuni da cewa a karshe zai daura aure da ita.

Davido ya kuma bayyana a cikin wata hira da Ndani a baya a cikin 2021, inda ya bayyana dangantakarsa da Chioma a bainar jama’a.

 

Daga Fatima Abubakar.