An samu rikicewa a filin saukan jiragen sama da ke Abuja a sanadiyar saukar gaggawa.

0
65

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka shiga firgita a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja lokacin da wani jirgin Max Air ya yi saukan gaggawa bayan da rahotanni suka ce tayar ta kama da wuta.

Jirgin dai ya taso ne daga Yola jihar Adamawa lokacin da lamarin ya faru.

Hukumar ceto da kashe gobara (ARFFS) da ke aiki a filin jirgin ta yi gaggawar daukar matakin kashe gobarar.

Tsohon shugaban kungiyar likitocin Najeriya (NMA), Dr. Mike Ogirima, wanda ya bayyana yadda lamarin ya faru, ya ce tayar jirgin ya samu matsala ne bayan tashin ta a filin jirgin saman Yola.

Sai dai jirgin ya yi saukan gaggawa ne a Abuja tare da jami’an bayar da agajin gaggawa don kashe gobarar kafin saukar fasinjojin a kan titin jirgin.

Ogirima ya ce, “Mun gode wa Allah. Har yanzu muna kan titin jirgi yadda matukin jirgi ya tabbatar mana. Ya kira stairs kuma yanzu muna sauka daga titin jirgin domin a kwashe mu zuwa ginin filin jirgin da ke zauren isowa.

“Mun yi wa Allah godiya saboda mun shaida yadda aka fiddo taya daga filin jirgin sama na Yola kuma nan take mu ka fara addu’o’i. Ya ce sun firgita sosai amma mun gode wa Allah.”

An sauke fasinjojin lafiya daga titin jirgin yayin da aka rufe titin na wani dan lokaci har sai an dauke  jirgin.

Wani jami’in kamfanin jirgin da ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce fasinjojin duk sun sauka lafiya.

Ya nuna godiya ga Allah da Ya tsare dukkan fasinjoji da ma’aikatan jirgin.

Ya ce kamfanin jirgin zai sanar da hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike kan lamarin.

…Daga Fatima Abubakar