DA DUMI DUMINSA:Harhashin bindigar sojoji da aka harba a runduna biyu ta Ibadan ya jikkata mutum biyu.

0
69

Wani hatsari ya faru a wasu yankunan da ke kusa da runduna ta biyu ta sojojin Najeriya a Odogbo a Ibadan yayin da wasu mutane biyu suka samu raunuka daga harbin bindiga daga cikin bariki.

An tattaro cewa daya daga cikin wadanda abin ya shafa mai kimanin shekaru 10 da haihuwa an bayyana sunan sa Daniel yayin da dayan kuma babba wanda aka fi sani da Baba Ajeri.

An ce an garzaya da wadanda abin ya rutsa da su zuwa asibiti da ke cikin bariki kuma an ce jami’an kiwon lafiya na sojoji ke du ba su.

Mazauna yankin sun  ce,harsashi ne ya same su su biyun a yayin da ake gwajin  harbe-harbe a ranar Juma’a.

Inda suka ce harbe harben ya shafi musamman rufin gidajen su inda wasun su suka llalace sakamakon harbin bindiga da aka harba daga wajen.

Daya daga cikin jagororin al’ummar yankin Alhaji Kareem Ijeru ya ce   sabon harbe-harben ya yi tsanani a daren Juma’ar da ta gabata, kuma jama’a da dama sun ajiye motocinsu a wajen gidajensu.

Ya ce m un shafe shekaru muna cikin haka. Sun sake farawa jiya kuma yayi muni sosai a daren

“Kowa ya zauna a gida kuma dukkanmu mun kwanta don gudun kada harsashi ya same mu a cikin gidaje. An ci gaba da harbe-harbe a safiyar yau, kuma abin takaici, an samu mutane biyu da suka jikkata.

“An garzaya da su asibiti a bariki. Harsashin da ya same Baba Ajeri ba a cire ba amma Daniel ya yi sa’a, an ce min wanda ya same shi an ciro.

“Mun gudanar da zanga-zanga, mun kai kara ga sojoji a lokuta da dama amma lamarin bai canza ba.”

Wani mazaunin unguwar, Ade Owolabi, ya ce da yawa daga cikin masu gidaje a yankin sun bar gidajensu domin bayar da hayar masauki a wasu wurare domin tsira da rayukansu.

“Wasu daga cikin mutanenmu sun kamu da cutar hawan jini sakamakon fargabar da suke yi. Amma ta haka ne za mu ci gaba da rayuwa cikin haɗari? Ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taimaka mana,” inji shi.

Jami’in yada labarai na runduna ta biyu ta Najeriya Laftanar Kanal Charles Ekeocha da aka tuntube shi ta wayar tarho ya shaida wa wakilinmu cewa ba ya nan amma zai kira idan ya dawo.

 

Daga Fatima Abubakar