EPL: Mun yi kewan Ronaldo – Ten Hag ya fada, bayan sun tashi wasa kunin doki da Chelsea

0
46

 

Kocin Manchester United, Erik ten Hag, ya ce ‘yan wasansa sun yi kewan Cristiano Ronaldo bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 da Chelsea ranar Asabar.

Red devils ne suka mamaye wasan farko, amma sun kasa sanya karfinsu a Stamford Bridge.

 

 Masu masaukin baki sun fara cin kwallo ta hannun Jorginho fenariti, kafin Casemiro ya zura kwallon da kai wanda ya tabbatar da sun samu rabon maki.

 

 An cire Ronaldo a wasan, bayan da ya tashi daga benci Old Trafford, yayin da United ta doke Tottenham da ci 2-0 a ranar Laraba.

Ten Hag ya shaida wa Sky Sports cewa: “Kamar yadda aka saba, shi [Ronaldo] na iya zura kwallaye kuma yana da kima a gare mu. Muna buƙatar shi, a bayyane yake kuma kuna ganin hakan ma a cikin wannan wasan. Zai iya gamawa, hakan a bayyane yake.

 

 “Ina jin na yi magana da yawa game da wannan lamarin. Bari mu mai da hankali kan wannan wasan, wasa ne mai kyau ga ƙungiyar ta kuma dole ne in yaba wa ƙungiyar ta.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho