Fada ne yabarke tsakanin Sarkin Waka Da Nafisa Abdullahi hakan ya sa ta janye daga shirin labarina

0
490

Mun samu jita-jitan cewa a wata  daya gabata ne rikici ya barke tsakanin Jaruma Nafisa Abdullahi da Naziru Sarkin waka wadda yakai ga fada harda zage zage.

Kamar yadda muka ji hakan Yafaru ne bayan wani dan matsala da suka kasa sasantawa a tsakanin su.

Sanadiyan hakan ne Sarkin waka wanda yana daya daga cikin masu shirya shiri mai dogon zango “Labarina” yasa aka canza Nafisa da take taka rawan Sumayya.

Amma har Yanzu bamu ji komai daga baƙin masu shirya shirin ba,  ita jaruma ta bayyana janye wan ta daga shirin a cikin wata wasika da ta aikawa Mai shirya shirin Aminu saira Kuma ta wallafa shi a shafin ta na facebook da Instagram.

Tuni wasu masoya kallon shirin suke sa ido  suga wacece zata maye gurbin Nafisa a matsayin Sumayya.

By: Firdausi Musa Dantsoho