Gwamnan Jihar Gombe Ya Taya Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa, Ganduje Murnar Cika Shekaru 74

0
19

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya taya Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje murnar cika shekaru 74 da haihuwa a ranar 25 ga watan Desamba.

A saƙonsa na taya murna, Gwamnan Jihar ta Gombe, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ya yaba da irin jajircewa da dabarun da Dr. Ganduje ke nunawa wajen ciyar da jam’iyyar APC da muradunta gaba da tabbatar da haɗin kai da ci gaba a cikinta, tare da ɗora ta bisa muradun sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu GCFR.

Ya kuma yaba da yadda tsohon Gwamnan Jihar ta Kano ya jajirce kan tsarin aiki tuƙuru, jajircewa, da jagoranci nagari, da kuma rawar da ya taka wajen ɗora jam’iyyar kan ƙwaƙƙwarar turba.

“A wannan lokaci na bikin cikarka shekaru 74 da haihuwa, mu ‘yan Jam’iyyar APC na Jihar Gombe, mun bi sahun ɗimbin masoyanka don girmama jajircewarka kan kyawawan tsarin aiki tuƙuru da sadaukar da kai ga aƙidar babbar jam’iyyarmu da ƙasarmu abar ƙaunarmu. Tasirin Jagoranci da hangen nesanka a cikin Jam’iyyar APC ya kasance na musamman yayin da kake tsara hanyoyin samar mata makoma mai albarka.”

Gwamna ya yi addu’a yana mai cewa “Yayin da kake murnar wannan gagarumin biki, muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara maka lafiya da hangen nesa, ya kuma ƙara maka hikimar ci gaba da jan ragamar babbar jam’iyyarmu da al’ummarmu abar ƙaunarmu ya zuwa kyakkyawar makoma”.

Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe

 

Hafsat Ibrahim