Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yakarbi Bakwancin Ministan Sadarwa ta zamani na kasa

0
29

Asafiyar wannan rana Mai Girma Gwamnan jihar Kano H.E Alhaji Abba Kabir Yusuf yakarbi Bakwancin Ministan Sadarwa ta zamani na kasa Dr. Bosun Tijjani a babban dakin taro na Coronation Hall dake fadar Gwamnatin ta Kano.

 

Mai Girma Gwamnan yanuna jindadinsa ga ministan bisa wannan ziyara inda kuma yatabbatar wa minista dacewa Gwamnatinsa ashirye take kuma tana maraba da dukkan wani cigaba da kwamntin tarayya zata kawo a fannin Sadarwa na zamani, inda Gwamnan yakara dacewa daga zuwan gwamnatinsa yadawo da babbar makarantar nan ta koyar da karatun kimiyar fasahar zamani ta Imformatic insutitute, dan ganin cigaban wannan bangare a fadin jihar Kano dama kasa baki daya.

Mai Girma Ministan yayi Godiya ga mai girma Gwamna bisa irin tarba tamusamman daya samu yayin wannan ziyara, inda nuna jindadinsa ga Wannan Gwamnati mai Albarka ganin yadda take kokarin taimawa Al,umar jihar kano musamman matasa dan samun wannan ilimi na sadarwa ta zamani wanda hakanne yasa mai Girma Gwamnan yabude wannan makarantar koyar da ilimin kimiyar zamani ta Imformatic Insutite dake garin karfi yankin karamar hukumar kura, wadda Gwamnatin data shude ta rufeta tadaina aiki baki daya.

HON SALISU MUHAMMAD KOSAWA.

SSA II ON SOCIAL MEDIA TO THE EXECUTIVE GOVERNOR OF KANO STATE, ALHAJI ABBA KABIR YUSUF.

 

Hafsat Ibrahim