Kowa yasan yanayin zafi da muke tsintar kanmu a ciki daga watan fabrairu zuwa watan aprilu.
Tsananin zafi dake sanya mana rashin jin dadi a jikin mutane, musamman yara. Hakan yasa muka kawo maku yadda yakamata a kula da yaro a lokaci na zafi haka.
Abubuwan da yakamata muyi domin kula da yaranmu a cikin wannan yanayi na zafi su ne
Yawaita yi masu wanka, kanar yadda muka sani, yawanci sau biyu a rana ake wa yara wanka,watau safe da dare, amman duba da yanayi na zafi damuke ciki, yakamata anayi wa yaro wanka akai akai, koma sau uku a rana, saboda tara zufa da zai iya janyo wa yaro kurajen zafi a jiki., ba jiki kadai ba, harta cikin gashin kai za a wanke domin hana zufa kwanciya a cikinsa.
Kuma ya kasance wankan da za ayi masu da shi marar dumi ne sosai. Saboda ba a bukatar yi wa yaro wanka da ruwan zafi sosai.
Sannan a daina saka wa yaro kaya mai nauyi lokacin zufa,,kayayyaki marasa nauyi sune ya kamata ana sanyawa yara domin samun iska yana shiga jikinsu. A rika bude windodi saboda bada damar shigar iska cikin gida inda yaran suke. Yin haka na taimakawa kwarai wajen ragewa yara jin gumi.
Shan ruwa abu ne mai muhimmanci, a rika bawa yaro ruwa yana sha sosai a cikin yanayi na zafin nan da muke ciki, haka na taimaka wa sosai wajen hydration a turance. Yaro ya samu yana shan ruwa ko wane minti goma sha biyar, a kiyasce .
Sai kuma rage masu fita cikin rana,ko wasa cikin rana, inhar fitar ba dole bace, toh ana son ana ajiye yara cikin gida ko inda yake da iska sosai da inuwa.
A rage bawa yaro abu mai zafi yasha, misali shayi ko kunu, a barshi ya dan huce kafin a bawa yaro, saboda ba a bukatan yara suna shan abu mai zafi cikin jikinsu, hakan zai iya sakasu suyi gumi ko zufa wanda zai iya janyo masu rashin jin dadi a jikinsu.
Daga Maryam Idris