Jerin shugabannin kasar masu kankantan shekaru a duniya

0
133

 

 

Jerin sunayen shugabanin mafi karancin shekaru a duniya ya kunshi manyan matasan shugabannin da ke mulkin kasarsu tun suna kanana.

 

Wasu daga cikin waɗannan shugabannin duniya ba kawai matasa ba ne amma suna da kankantar shekaru fiye da wasu. Duk da haka, a duniya a yau, kusan dukkanin shugabannin sun tsufa sosai.

Saboda kasancewar yawancin shugabanin kasa masu shekaru sun fi yawa, mutane suna tunanin cewa babu shugaban kasar da bai kai shekara 50 ba.

 

A cikin wannan jerin shugabannin kasa zamu kawo maku yan kasa da ko kuma na kusa da shekaru 50. Lokacin da mutane ke cewa matasa ne shugabannin gobe, babu shakka a kan hakan domin kasashe da yawa suna zabar matasa a matsayin shugabanni.

  1. Giacomo Simoncini

Giacomo Simoncini shi ne shugaban kasa mafi karancin shekaru a Duniya kuma shi ne kadai shugaban kasa kasa da shekaru 30. Ya kasance ɗan siyasa kuma ɗaya daga cikin Kyaftin Regent wanda ya yi mulki tare da Francesco Mussoni daga 1 ga Oktoba 2021 zuwa 1 ga Afrilu 2022.

Duk da haka, an haife shi a ranar 30 ga Nuwamba 1994 kuma a shekara ta 2021 yana da shekaru 27. Haɗin gwiwa na watanni shida ya fara a ranar 1 ga Oktoba 2021.

Ya kasance shugaban jiha mafi karancin shekaru a duniya, kuma shine kadai shugaban kasa kasa da shekaru 30 daga 1 ga Oktoba 2021 zuwa 1 ga Afrilu 2022

  1. Sanna Marin:

Sanna Mirella Marin matar Markus Räikkönen ita ce shugaba na biyu mafi karancin shekaru a duniya. Ita ‘yar siyasa ce Finnish wacce ta yi aiki a matsayin Firayim Minista na Finland tun 2019.

An haifi firaministan kasar Finland a ranar 16 ga Nuwamba 1985. A wanan shekaran tana da shekaru 36.

Kafin ta zama Firayim Minista na Finland, ta kasance ministar sufuri da sadarwa a Finland.

Duk da haka, ita memba ce ta Social Democratic Party of Finland, ta kasance ‘yar majalisa tun 2015.

  1. Kim Jong-un :

Dan siyasar Koriya ta Arewa kuma shugaban kasar Kim Jong-un mai shekaru 38 na daga cikin manyan shugabanni 5 mafi karancin shekaru a duniya. Kim Jong-un ya kasance shugaban koli na Koriya ta Arewa tun shekara ta 2011.

Duk da haka, shi dan Kim Jong-il ne, wanda shi ne shugaban koriya ta Arewa na biyu daga 1994 zuwa 2011, da Ko Yong-hui.

An haife shi a ranar 8 ga Janairu 1984 a Wonsan, Koriya ta Arewa yana da shekaru 38 a halin yanzu.

Haka kuma, ya zama shugaban kasa a shekarar 2011 yana dan shekara 21. Baya ga kasancewarsa cikin manyan shugabannin duniya, yana daga cikin manyan masu kudi da tsoro a duniya.

  1. Assimi Goita:

Kanar Assimi Goïta jami’in soja ne na kasar Mali wanda ke rike da mukamin shugaban rikon kwarya na kasar Mali tun daga ranar 28 ga Mayun 2021.

Goïta shi ne shugaban kwamitin ceto al’umma na kasa, gwamnatin mulkin soji da ta kwace mulki daga hannun tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keïta a juyin mulkin 2020 na Mali.

Assimi Goita, wanda aka haifa a shekara ta 1983, kuma a halin yanzu yana da shekaru 39 a duniya, yana cikin shugabannin Afirka mafi karancin shekaru.

dan wani hafsan sojan kasar Mali, ya samu horo a makarantun soji na kasar Mali, kuma ya halarci Prytanée Militaire de Kati da kuma makarantar hadin gwiwa ta sojoji a Koulikoro.

Sai dai Goita shi ne shugaban kwamitin ceton al’umma na kasa, kungiyar ‘yan tawayen da ta hambarar da Ibrahim Boubacar Keta a juyin mulkin Mali na shekarar 2020 tare da sha alwashin gudanar da sabon zabe domin maye gurbinsa.

Kafin ya zama shugaban kasa Goita ya rike mukamin Kanal a bataliyar sojojin kasar Mali mai cin gashin kanta. A lokacin shi ne Kanal mai kula da dakarun musamman na kasar Mali a tsakiyar al’ummar kasar

 

  1. Irakli Garibashvili:

Daga cikin manyan shugabannin duniya akwai firaministan Jojiya Irakli Garibashvili. Irakli Garibashvili ya na hidimar Jojiya tun 22 ga Fabrairu 2021

Irakli Garibashvili ɗan siyasan Jojiya ne, kuma firayim ministan Jojiya tun daga 22 ga Fabrairu 2021. Ya yi aiki a matsayin firayim minista daga 20 Nuwamba 2013 har sai da ya yi murabus a ranar 30 ga Disamba 2015 kuma tsohon shugaban kasuwanci ne, Yana da shekaru 40 a yanzu.

 

Daga:Firdausi Musa Dantsoho