Kayattattun Hotunan  Kafin Biki Na Yusuf Buhari Da Zahrah Bayero

0
338

Da namiji tilo guda ga shugaban kasan nijeriya Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari zai auri iyar sarkin Bichi Nasir Ado Bayero, Zahra Bayero.

Daurin auren da za’ayi shi karshen wannan makon, ranar 20th ga watan augusta, a jihar kano.

A wannan satin ne sarkin Bichi ya nuna damuwansa akan rabuwa da iyarsa bayan ta auri dan shugaban kasan nijeriya.

Mai martaban ya bayana cewa abune mai wahala a gareshi ya aurar da iyarshi sabida kusancinsu.

Amma duk da hakan yayyi wa Yusuf da Zahra fatan zamantakewan aure mai albarka.

Ya kara da cewa duk wadda yayyi rainon iyayya mata uku har ya aurar dasu yana da gida a Aljanna.

Ga hotunan ango Talban Daura Yusuf Buhari da Amaryansa gimbiya Zahra Bayero: