YADDA AKE  HADA MIYAN CREAMY CHICKEN SOUP

0
221

Creamy chicken soup miya ne da  yake da saukin hadawa ga daddi kuma baya bukatan kasha kudi domin hadasa.

Shi wannan miyan yana da daddin sha zallan shi  musamman a wannan lokacin sanyi ana kuma iya hada shi da farar shinkafa,farar taliya ko macroni.

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

 • Zallan tsokan kirgin kaza
 • Karas
 • Peas
 • Green beans
 • Masaran gwangwani
 • Butter
 • Flawa
 • Madaran ruwa
 • Sinadaran dandano
 • Ganyen celery
 • Gishiri

YADDA AKE HADA MIYAN

 1. Zamu yanka tsokan kirjin kazan mu kanana sai mu zuba gishiri da sinadarin dandano mu tafasa.
 2. A wani tukunya mu sa butter idan ya narke sai mu zuba karas,peas da masaran gwangwani mu a ciki mu dan soya,
 3. Sai mu zuba flawa mu aciki mu juya zamu gan cewa flawan ya kama jikin suk karas in kuma ya shanye butter in.       
 4. Sai mu zuba ruwan madaran mu mu juya,sai mu dauko ruwan da muka tafasa kazan mu mu kara aciki.
 5. Sai mu zuba tsokan kazan mu, sinadaran dandano, ganyen celery,garin tafarnuwa,garin citta,da masoro mu juya sai mu barshi na minti 3.
 6. Bayan minti uku creamy chicken soup inmu ya hadu. Asha lafiya

 

By: Firdausi Musa Dantsoho