Kwadon Zogale.                 

0
555

 

 An ce zogale yana taimakawa rage yawan sukari na jini kuma yana taimakawa rage matsalolin da suka shafi ciwon sukari. Hakanan yana taimaka rage ƙona da taimakawa Wajan rage kiba.

Haka kuma an ce zogale yana kare kai daga kamuwa da kwayoyin cuta, fungal da cututtuka, yana taimakawa lafiyar hankali, fata da gashi da tsufa.

Lokacin cin sassan tsiron zogale, ana ba da shawarar ku san duk wani magani da za ku sha wanda ke da fa’ida kamar ta zogale.           

Shiyasa Ayau zamu koya maku yadda zaku kwada zogalen ku, kuma ku ji dadin cinsa domin samun fa’idar sa.

Abubuwan bukata sune:

 

*Ganyen zogale kamar yadda ake bukata

* Gurji (cucumber)

*Tumatir

*Barkono

*Baprika

*Albasa

*Mai

*Kayan yaji

*Kuli kuli kamar yadda ake buƙata.                   

 *Sinadarin dandano.           

Matakan Hada Kwadon Zogale

  1. Da farko za’a Cire ganyen zogale daga tushe kuma a wanke sosai, a dafa a cikin tukunya na mintuna 20-25 har sai ya dahu sosai.
  2. Sannan a yanka su tumatir, cucumber, albasa  duk kayan marmari sosai, sannan a juye zogalen da aka dafa a cikin babban kwano, sai mu zuba  kayan lambun mu da muka yanka, mai, kayan yaji, sinadarin dandano dan dai-dai da kuli kuli da yawa, sai a gauraya sosai, Toh kwadon Zogalen mu ya hadu. 

       

Abun lura: zaku iya shan ruwan da aka dafa zogalen shima yana da matukar amfani.         

  By: Firdausi Musa Dantsoho