Abaya dogon riga ne dake haska kwalliyan mata na yau da kullum. Abaya kwalliya ne da mata keson shi mussamman a zamanin mu na yau saboda tufafi ne dake rufe jikin diya mace daga sama har kasa harma da hannayenta.
Abaya yasamu asali ne daga kasashen larabawa wanda hakan ya baiyanar da kalmar Abaya. Inda matan larabawa ke kwalliyansu dashi. Abaya riga ne da musulmai ke anfani dashi a kasashen duniya wanda suke ganin shine mafi saukin kaya wajen rufe jikinsu gaba daya. Haka zalika wadanda ba musulmai bama sun kasance suna saka abaya sabida saukin shi da kuma kasan cewarshi kaya mara nauyi kuma kaya ne mai rufe tsiraicin jiki.
Abaya ayau ya zama tufafi daya zaga duniya gaba daya wanda wanda har a kasarmu ta Nigeria an dauketa a matsayin tufafi na mutunci da kuma kamala domin yadda ya kasance abun rufe jiki ga mata.
Abaya dogon riga ne wanda ake kawatashi da kwalliya, wasu na da duwatsu wasu na da zubin zare wasu kuma plain.
Abaya yawancinsu bakine amma kwalliya irin na zamani yasa akwai wasu launika daban daban wanda ake kira da Arabian gown. Amma de Abaya yakasu kala daban daban Akwai wanda ake kira After dress wanda ake sawa indan ansaka kaya na musamman aciki ko kana nan kaya sai a daura shi akai.
Akwai kuma dogon riga wanda gaban a rufe yake bakaman after dress ba, shi ana sakashi ne a matsayin riga mai zaman kanshi.
Sai kuma Arabian gown wanda shima kaman Abaya yake kawai shi azamanin mu na yau dazo da styles nashi da launika daban daban yasa mutane ke kiran kayan da arabian gown. Abaya a zamanin mu na yau akwai din kuna da ban da ban.
Akwai wanda akeyinshi mai dinkin fuka fukai wato dinkin irin na butterfly wanda ake kira da malam bude takarda.
Akwai wanda yake dogo mai shape wasu kuma suke kara saka shape din dan yakara kawata kayan da kwalliyan su. Daga sama shape din yake kasan kuma yake abude.
Akwai wanda ake yi masu belt mai fadi ko siriri.
DAGA:RUKAIYA UMAR DIGMARI