LEMUN TSAMIYA

0
721

Tsamiya na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwa da Al’ummar Hausawa ke amfani dasu sosai a rayuwar su ta yau da kullum.Tana da amfani mai tarin yawa. Ana  sarrafa tsamiya a matsayin kayan sha, inda a yau wajaje dadama wasu kan qullata a leda ko gora bayan sun taceta sun gaurayata da sukari sai su sakata a na’urar sanyi(refrigegrator) wadda ayau haka zamu koya maku.

Wasu kuma sun dauketa a matsayin magani da kuma sarrafata a matasyin abinci domin akan yi kunun tsamiya da kuma tuwon tsamiya a wasu yankunan arewacin nijeriya.

ABUBUWAN BUKATA: 

*Tsamiya

*Citta

*Kaninfari

*Mazarkwaila ko siga

*Abarba

 YADDA AKE HADAWA

  1. Da farko Ki jika tsamiyarki idan ya jiku sai ki juye a tukunya ki xuba citta d kaninfari ki tafasa sai ko tace idan ya huce.
  2. saiki markade abarban ki ki tace ki zuba a cikin lemun tsamiya.

3. Daga nan saiKi saka mazarkwaila ko siga ki gauraya sai ki saka a fridge yayyi sanyi asha lafiya.

 

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho