Magance FasoDa Kaushi A Lokacin Sanyi

0
186

 

Tafin kafa sassan jiki ne da ke bukatar kulawa na musaman, sanyi na busar da shi yakuma sa shi kaushi har ya zama faso in ba a magance kaushin da wuri ba. Kaushin kafa na kama kaya mai aduga da sa wanan kayan gashi. Kaushi da faso na rage wa mace aji da nuni da rashin kula.

Yana da kyau a san hanyoyi da yadda za’a kula da kaushi da fason kafa.

Kayan amfani

●Shamfo
● Gishiri
● Dutsen goge kafa
● Baho mai fadi
● Moisturizer, man kadanya ko man mayuka

A zuba ruwan dumi a baho, Shamfo murfi biyu, gishiri rabin cokali sai a juya a saka kafafuwa a zauna na minti 30 zuwa arba’in don su juku da kayau. Bayan nan a dau dutsen goge kafa a goge, zai fitar da matacen fata da ya juku sai a dauraye da ruwa sanan a shafe su da mai.

Za’a iya amfani da abun goge kafa na turawa don fida kaushin kafa kafin a shiga wanka, yin amfani da wanan kulum ko duk bayan kwana biyu zai rage kaushin kafa.

Daga Safrat Gani