Najeriya Ta Kammala Gasar Wasannin Olympics na Paris Ba Tare da Lambobi ba.

0
15

Najeriya ta ƙarkare Olympics ta Paris ba tare da samun lambar yabo ko ɗaya ba

Duk da yadda gwamnatin Najeriya ta kashe makudan kuɗade har Naira biliyan 12 kan ƴan wasanta su 82 , wadanda suka halarci gasar data kunshi guje-guje da tsalle-tsalle a Olympics, Wanda aka gudanaf a birnin Paris na kasar Faransa.

To sai dai ƴan wasan ƙasar sun kammala wasannin ba tare da samun lambar yabo ko guda ɗaya ba.

Wanda tuni wannan batu ya haddasa kakkausar suka daga ɓangarori daban-daban musamman masu sanya idanu kan yadda harkokin wasanni ke gudana.

Amman an bayyana Rashin samun lambobin yabo a gasar ta Olympics a matsayin babban koma baya ne ga ɗaiɗaikun ƴan wasan dama tarin tawagogin na Najeriyar wadanda da aka yi tsammanin zasu haska matuƙa a wannan gasa da bisa al’ada suka saba nuna bajintarsu.

WAIWAYE

Rabon Najeriya da nuna bajintar azo a gani a wannan gasa tun A shekarar 1996.

To saidai mahukunta sun magantu inda ministan matasa da wasanni na Najeriya John Enoh ya ce”Dole mu yi wa ƴan Najeriya bayani game da komai ” ma a na Yan Nageriya su bimu bashi, dukkan bayanin yadda Al amuran dama halin da ƴan wasan ƙasar suka fuskanta a birnin Paris.

Idan zaku tuna tawagar Yan Nigeria sun fuskanci kalubale da dama , ciki kuwa har da batun Ƴar wasan Najeriya Ofili ta kafa sabon tarihi a gasar Olympics.

JADAWALIN GASAR

Ƴan wasa 10,714 suka halarci gasar da aka yi wasanni daban-daban har guda 329, fitattun daga cikinsu 32 ne Kuma anyisu a fannoni 48.

Tawagar Amurka ce ta lashe gasar ta bana da lambobin yabo mafi yawa, inda ta kwashe zinare 40, da azurfa 44 da kuma tagulla 42, duka Jummalar ya kama 126.

ABIN SHAAWA

Ƙungiyar ƙwallon ƙwando ta mata ta Amurka ta taimaka wajen ganin kasarsu ta samu nasara a gasar inda ta doke Faransa mai masaukin baƙi tare da lashe lambar zinare ta karshe a gasar.

China

Tawagar ƙasar China da ke yankin Asiya ke biye mata da yawan lambobin azurfa 44. Inda ta sami 27 tagulla 24, Jummalar 91.

Japan

Tawagar Kasar Japan ce ta uku da zinare 20, sai azurfa 12 dakuma tagulla 13 inda a Jimlance suke da 45,

Australia

yayin da Australia ta zo ta hudu da zinare 18 sai azurfa 19 dakuma tagulla 16 , inda jumulla tana da 53.

France

Faransa mai masaukin baƙi wacce ta kasance a matsayi na biyar , tasamu zinare 16, da azurfa 26, da Kuma tagulla 22, inda a jimilla ta na da 64.

Daga yankin Afrika kuwa:ƙ

ungiyoyin Afirka 12 ne suka samu damar lashe lambobin yabo.

Kenya

Tawagar Kenya ce ta jagoranci nahiyar, bayan ta samu zinari hudu da azurfa biyu da Kuma tagulla biyar, jimillar 11. Kuma ta kare a matsayi na 17.

Sauran kasashen Afirka da suka samu lambar yabo sun hada da Aljeriya wadda ta samu zinari biyu da tagulla daya uku jumulla.

Afirka ta Kudu a matsayi na 44 tare da jimlar lambobin yabo shida wadanda suka hada da zinari 1, azurfa 3, tagulla 2

Sai Tawagar Habasha wadanda suke da zinare 1 dakuma azurfa 3. Kuma sune a matsayi na 47 .

 

 

Hafsat Ibrahim