Rundunar yan sandan Najeriya sun kai samame a Dawaki da Dutsen Alhaji tare da rusa maboyar wasu masu aikata miyagun laifuka.

0
73

Tawagar runduna ta biyar ta rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja, a daren Laraba, ta tarwatsa wata maboyar da ke unguwar Dawaki shiyya ta 7 a Abuja, yayin da ‘yan bindigar da ke maboyar suka tsere bayan sun ga ‘yan sandan.

Wakilin ya tattaro cewa maboyar da ke a shiyyar Dawaki ta 7 tana dauke da ’yan bindigar da ke addabar yankunan Dawaki da Dutse Alhaji na babban birnin kasar.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce maboyar ta kasance wata matattarar masu aikata laifuka, inda ya kara da cewa mazauna garin na kaffa-kaffa da wurin musamman da daddare.

Rundunar ‘yan sandan da suka fito daga sashin Dawaki, Zuba, Kubwa, Bwari, da Dutse Alhaji ne suka kai samame a majami’ar, karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda na  Dawaki, SP Ali Johnson.

Wani jami’in ‘yan sanda wanda kuma ya zanta da wakilinmu da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa an rusa sansanin ne domin hana ‘yan ta’addan sake haduwa tare da mayar da maboyar zuwa wurin aikata laifuka,

Ya ce, “’Yan iskan, da suka ga tawagarmu, ba su yi kasa a gwiwa ba. Don haka ba mu da wani zabi illa mu kona maboyar.”

Da take tsokaci kan aikin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan FCT, Josephine Adeh, ta ce farmakin na wani bangare ne na kokarin da rundunar take yi na kakkabe duk wani mai laifi a cikin babban birnin kasar.

Adeh ta ce, “Muna lalata tare da toshe kowane bangare don tabbatar da cewa mun kawar da duk wani mai laifi a cikin babban birnin tarayya.

 

Daga UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.