Soyayyah wata abu ce mai wanzar da nutsuwa a zuciyar mai yinta, wata abu ce Mai dadin gaske wacce dadin ta bashi misaltuwa kuma bashi faduwa a baki sai dai a kwatanta, musamman idan kayi gam da katar ga Wanda kake so kuma yake son ka.
Sai dai idan ka so Kuma ba’a so ka ba fa , wannan shi ake Kira son ma so wani.
Shin Ko menene son maso wani?
A takaice son ma so wani shine, ka so a qi ka, kabi abi wanin ka, kayi kokarin faranta ran Wanda kakeso shi/ita kuka Yana kokarin faranta ran wani daban. Babu abu Mai wahal da ruhi da gangar jiki sama da son ma so wani domin sau tari za kaga Wanda kake bi Yana bin wani Wanda wata Kila ma Bai Kai ka komai ba, ka fishi kyan gani, arziki, iya saka kaya da komai sai dai Kuna masu iya magana sunce shi so makaho ne ba gani yakeyi ba balle kyakyali, akwai zafi matuqa ga masoyin da zaiyi duk abinda zaiyi domin ya faranta ran abinda yake so Amma a maimakon haka sai dai ya bakanta, shi duk abinda kayi na birgewa a idanun Wanda kake so baya gani domin ba da idanu masoyi yake gani ba, da zuciya ne.
Idanun masoyi abu guda kawai yake gani, shine wanda yake so. wannan shine dalilin da mai so a so shi yake rayuwa cikin qunci domin duk nau’in kyautatawa da farantawa yanayi amma amman ba’a gani kuma babu abu mai baqanta rai sama da kayi abun a yaba ka amma Kuma a kushe ka musamman wajen masoyin da kake so.
Sannan ba abinda ke kawo kushe kamar ka so mai son wanin ka, Ina nufin son ma so wani.
Wasu ma sukan ce, Son ma so wani wani yanki ne daga yanki azaba, domin yafi wuta kuna sannan Kuma yafi madi daci.
Daga Maryam Idris