YADDA AKE HADA GARIN KUNUN TSAMIYA DA KUNUN TSAMIYA

0
2085

Yin garin kunun tsamiya wanni hanya ne da zaku bi domin rage wa kanku aiki, shi de kunun tsamiya kunu ne da yake da dadi ga saukin yi kuma ana amfani da tsamiya ne wajan hada shi.

Ayau a shafin mu na tozali zamu koya maku yadda ake hadda garin kunnun tsamiya das hi kunun tsamiyan.

ABUBUWAN BUKATA WAJAN HADDA GARIN SUNE:

  • Gero
  • Kanunfari
  • Masoro
  • Barkonu
  • Busasshen citta

YADDA AKE HADDA GARIN KUNUN TSAMIYAN

  1. Zamu fara da wanke geron mu tas, sai mu shanya shi ya bushe.
  2. Sai mu zuba su kayan kamshin mu su, kanumfari, citta, barkonu, masoro, mu kai nika .
  3. Mu tabbattar enjin babu ruwa kuma za,ayi mana nikan gari ne.
  4. Toh garin kunun tsamiyan mu ya haddu.

YADDA ZAMU HADDA KUNUN TSAMIYAN MU

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

  • Garin kunun tsamiya
  • Tsamiya
  • Siga ko zuma
  1. Zamu wanke tsamiyan mu, sai mu jika idan ya jiku sai mu tace a cikin tukunya mu kara ruwa mu barshi ya tafaso.
  2. Idan ya tafaso sai mu kwaba garin kunun tsamiyan mu da ruwa ya dan yi kauri ba sosai ba.                                                                 
  3. Sai mu zuba ruwan tsamiyan daya tafasa a cikin kwabin garin kunun tsamiyan .
  4. Idan kunun ki baiyi kauri ba zaki iya mai dashi kan wuta ki yi ta juyawa har sai yayyi kauri, da zaran kunun ki yayyi kauri to kunun tsamiyan ki ya hadu
  5. Sai a zuba siga ko zuma asha lafiya

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho