YADDA AKE HADA CHOCOLATE MILK SHAKE

0
635

 

 

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

  • Kankara ( ice cubes)
  • Chocolate ice cream da vanilla ice cream ludayi daddaya
  • Madaran ruwa kofi daya
  • Sigar cokali biyu
  • Coco powder cokali daya
  • Milo cokali daya

YADDA AKE HADAWA

  1. Da farko zaki yi wa kofinki ado da chocolate syrup kisa a fridge.
  2. A cikin abun markaden ki watto blender ki zuba kankara,ice cream, madaran, ruwa, coco powder, da milo ki markade su gabaki daya.     
  3. Idan ya markadu sai ki fito da kofin ki daga cikin fridge ki juye a ciki.
  4. Zaki iya kara masa ado da whipping cream idan kina so idan ba kai so toh asha lafiya.

 

By: Firdausi Musa Dantsoho