YADDA AKE HADA NAGARTACCEN KUNUN AYA (TIGERNUT DRINK)

0
636
Kunun Aya na daya daga cikin abun sha mai farin jini sosai ba a nan kadai arewacin nigeria ba ,a qasar gaba daya. Ana yin kunun aya ne daga Aya (tiger nuts) . Yana da dadin sha da sanyaya jiki da makogwaro.
Abubuwan da ake bukata domin hada kunun aya sune kamar haka.
– Aya
– Madara
– Kwakwa
– Dabino ( busashe)
– Citta
– Sugar
-Rake (sugar cane)
– Flavour
Yadda ake hadawa; 
Da farko za mu debo Aya daidai yadda ake bukata a jika ta. In ayar ta jiku sai a wanke a rairaya a cire kasa da kananan duwatsu. Sai a bare dabino mai dan yawa a cire kwallon a zuba a kan Aya din. Sai a babbala rake da wuka a zuba,Sai a saka citta akai nika.
 A bare kwakwa a gurza  a grater sai a saka a blender a nika sosai, in an kawo kullun ayar da aka nika sai a hada da wannan kwakwar a kara ruwa a tace su, sai a saka flavour da aka fi so, (Banana flavour yafi dadi) da sugar.  Wasu sukan matse ruwan rake su zuba basu sakawa a nika su tare kamar yadda nafada daga farko.
Mu sani cewa kunun Aya na son sanyi sosai,,saboda haka kullum ya kasance cikin sanyi domin yana saurin lalacewa kuma bata da dadin sha in babu sanyi sosai.
Daga Maryam Idris